Kasar Turkiya Ta Sake Kai Wani Sabon Hari A Arewacin Kasar Iraqi.
A yan shekarun baya bayan nan kasar turkiya ta kai hare-hare cikin kasar Iraqi ta da sunan dakile hare-haren kungiyar Kurdawa ta PKK dake kasar, sai dai harin ya fuskanci mayar da martani mai tsananin daga Gwamnatin Iraqi da ma wasu kasashen duniya.
Tashar talabijin din Sumeria ta kasar Iraqi ta bayyana cewa A daren jiya ne dakarun sojin kasar Turkiya suka kara kai hari kan kauyen Amedi dake lardin Dohuk a Arewacin kasar Iraqi, kuma ya zo ne bayan da a makon jiya mana wasu fararen hula guda 9 suka rasa ransu wasu guda 23 kuma suka jikkata sakamakon har da sojojin suka kai a garin Dohuk
Ana sa bangaren Fira ministan kasar Iraqi Mustapha Kadhimi ya yi tir da kai harin kuma yace kasarsa na da hakkin kare kanta ko mayar da martani kan keta huruminta da kasar Turkiya ke yi.
READ MORE : Rashin Tabukawar Kwamitin Tsaro Na Karawa Isra’ila Karfin Guiwar Ci Gaba Da Zaluntar Falasdinawa.
A wani labara kuma an kai hari da makamin roka kan ofishin jakadancin turkiya dake garin Musel na kasar Iraqi a daidai lokacin da zaman tankiya ke kara kamari tsakanin Iraqi da Turkiya.
READ MORE : Kasar Oman Na Goyon Bayan Iran Kan Halattaccen Hakkinta Na Neman A Cire Mata TaKunkumi.