Shaihun malami a tsangayar ilimin siyasa, kuma daraktan cibiyar nazarin dokoki a jami’ar Abuja ta Najeriya farfesa Sherrif Ghali, ya ce har kullum, Kasar Sin a shirye take ta taimakawa kasashen Afirka, a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula. Kamar dai yadda Sin din ta nuna hakan, yayin taron kwamitin tsaron MDD na baya bayan nan.
Shaihun malamin ya ce, Kasar Sin ta nuna cikakkiyar ’yan uwantakar dake tsakanin ta da kasashen Afirka, a gabar da sassan biyu ke wakilta, da taimakawa juna a mataki na MDD. Don haka Sin ta yi abun da ya dace dukkanin manyan kasashen duniya su yi.
Farfesa Sherrif Ghali ya ce “Muna fatan ganin an aiwatar da hadin gwiwa mai ma’ana tsakanin sassan kasa da kasa, ta yadda hakan zai taimakawa Afirka, wajen shawo kan annoba, da bunkasa farfadowar tattalin arzikin nahiyar, tare da warware kalubalen ci gaba da na tsaro dake addabar ta. (Saminu Hassan).
Kasar sin tana zaman kasar da ta samu karbuwa sosai a najeriya idan aka kwatanta da kawar ta Iran wacce take fama da matsalolin bayanan nuna kiyayya daga kungiyoyin wahabiyawa wadanda akasari masu goyon bayan ta’addanci ne kuma suna samun tallafi daga saudiyya.
Ana fat ar najeriya ta amfana da kasashen duniya irin su Iran bayan an kawo karshen matsalolin kungiyoyin wahabiyawa masu tsatstsauran ra’ayin ta’addanci wanda ya saba da koyarwar addinin musulunci sahihiya.
Kasar Sin dai ta ciki tuta a bangaren sauyen al’adu tsakanin ta da najeriya ta fannoni da dama wanda hakan ke nuna tsari mai kyau da Sin din take dashi dangane da kyautata alaka da Najeriya ba tare da wata matsala ba.
A kwai alakoki musamman na kasuwanci tsakanin Najeriya da Sin wanda kuma alakar tayi karfi sosai da sosan gaske, hakan kuma abin yabawa ne musamman idan akayi alakar domin taimakon ‘yan kasuwar najeriya.