Kasar Sweden Ta Bayyana Bukatarta Ta Shiga Kungiyar Tsaro Ta NATO.
Kasar Sweden Ta Bayyana anniyarta na shiga kungiyar tsaro ta NATO bayan da mafi yawan yan majalisar dokokin kasar suka amince da hakan. Da wannan kuma kasar ka kawo karshen adawa da shiga kungiyar wacce jam’iyyar social Democratic mai mulkin kasar ta yi ta nunawa a baya.
Kamfanin dillancin lanaran reuters ya bayyana cewa yakin da aka fara a kasar Ukrain na daga cikin abubuwan da suka canza ra’ayin yan majalisar dokokin kasar a baya-bayan nan.
Banda kasar Holanda kasar Finland ma tana kan hanyar gabatar da bukatarta na shiga kungiyar tsaron.
Labarin ya kammala da cewa a jiya Lahadi 15 ga watan Mayu ne majalisar ta gudanar da taron amince da bukatar shiga kungiyar tan NATO.
Kasashen Turai na gabas fiye da 10 ne suka shiga kungiyar Tsaro ta NATO tun bayan rushewar tarayyar Sovied a shekara ta 1991. Kafin rushewar tarayyar dai gwamnatin kasar Rasha ta kasashen yamma kada su fafa kungiyar Nato daga kasashen gabacin Turai.
READ MORE : Takobin kisa bai tsaya a Saudiyya ba.
Day daga cikin dalilanyakin Rasha a ukrain sun hada da jinine batun shiga kungiyar tsaro ta Nato.
READ MORE : Muhammad bn Zaid; Daga mai mulki a bayan fage zuwa fadar shugaban kasar UAE.