Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasarsa za ta bayar da karin gudunmawar alluran rigakafin COVID-19 miliyan 100 ga kasashe masu tasowa a bana, baya ga gudunmawar dala miliyan 100 da za ta ba shirin COVAX.
A cewarsa, Sin za ta yi kokarin samar da allurai biliyan 2 ga duniya zuwa karshen bana. Yana mai cewa, zuwa yanzu, Sin ta samar da allurai sama da biliyan 1 ga kasashe da hukumomin kasa da kasa sama da 100.
A wani labarin na daban yau da safe ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na Amurka Joe Biden ta wayar tarho bisa gayyatar da ya yi masa, inda shugabannin biyu suka yi musanyar ra’ayoyi kan abubuwan da suka jawo hankalin sassan biyu.
A halin yanzu, dalilin da ya sa huldar dake tsakaninsu ta shiga mawuyancin yanayi shi ne yadda gwamnatin Amurka ta mayar da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba, da yadda take daukar matakin da bai dace ba domin matsa wa kasar Sin lamba, a don haka idan Amurka tana son kyautata huldar dake tsakaninta da Sin, dole ne ta canja manufar da take aiwatarwa kan kasar Sin, ta daina mayar da kasar Sin a matsayin kalubale ko abokiyar gaba, haka kuma ta daina gurgunta ikon mullki da tsaro da kuma moriyar ci gaban Sin.
Alamu dai suna nuna babu yadda za’ayi a samu daidaito tsakanin amurkan da sin sakamakon bambantar maslahohin juna.