A bana an cika shekaru 50 da maido da halastacciyar kujerar wakilcin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD.
Cikin wadannan shekarun 50 da suka gabata, kasar Sin ba kawai ta yi nasarar samun ci gaban kanta ba ne, har ma ta kasance kasa mafi bayar da gudunmawa ga ci gaban duniya.
Karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin ta cimma nasarar kawar da talauci karkashin ajandar samar da dawwamamman ci gaba na MDD nan da shekarar 2030, wato kasar ta cimma wannan muradin shekaru 10 gabanin cikar wa’adin da MDDr ta kebe, lamarin da ya bayar da gudunmawar sama da kashi 70% na rage talauci a duniya baki daya.
Kafin shekaru 8 da suka gabata, kasar Sin ta bijiro da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta riga ta samu kyawawan martani daga kasashen duniya 140 da kungiyoyin kasa da kasa 32.
A cewar wani rahoton bankin duniya, ya zuwa shekarar 2030, ana kyautata zaton shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta taimakawa mutane miliyan 7.6 a fadin duniya wajen tsame su daga kangin talauci, kana wasu mutanen kimanin miliyan 32 za su yi ban kwana daga matsakaicin talauci a fadin duniya.