Ma’aikatar tsaron kasar Sin, ta bayyana adawa mai karfi dangane da furucin da ministan tsaron Australiya Petter Dutton, ya yi game da kasar.
Wu Qian ya ce furucin Dutton, ya bayyana tunaninsa na bangaranci da kaddamar da yakin cacar baka, wanda ba zaman lafiyar duniya da ci gaba da hadin gwiwa kadai ya ke wa barazana ba, har ma da illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin da ma muradun ita kanta Australiar.
Wu Qian ya jadadda cewa, kasar Sin na kiyaye hanyar samun ci gaba cikin lumana da kuma manufar tsaron kasa bisa kariya.
Ya ce kasar Sin ba ta zaman barazana ga kowacce kasa, kuma bunkasa rundunarta na soji baya nufin ta yi hakan ne domin wata kasa.
An kaddamar da dandalin taron hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu da dandalin taron raya rukunin masana’antu tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, wanda zai gudana daga jiya zuwa yau, 11 ga wata a Nanning, fadar mulkin lardin Guangxi dake kudancin kasar Sin.
Yayin taron dandalin, an shirya bikin daddale kwangilolin ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, inda aka daddale kwangiloli 36 a zahiri da kuma kafar yanar gizo, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 20.
Babban taken dandalin shi ne “ingiza hadin gwiwa ta hanyar raya rukunin masana’antu bisa sabon tsarin samun ci gaba”, kuma makasudin shirya taron dandalin shi ne, sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren samar da kayayyaki bisa shawarar ziri daya da hanya daya ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa, da kuma moriyar juna.