Kasar Rasha Za ta Yanke Wutar Lantarki Da Take Bawa Kasar Finland.
Rahotanni sun bayyana cewa mai yi yu wa ne kasar rasha ta dakatar da wutar lantarki da take bawa kasar Finland a wannan makon bayan da kasar ta nuna aniyarta ta amincewa ya shiga cikin kawancen soji na Amurka da kungiyar tsaro ta neto a tsakiyar rikicin kasar rasha da Ukrain.
Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar rasha ya danganta batun dakatar da bada wutar lantarki ne saboda rashin biyan takudade na watan mayu, sai dai masana sun nuna cewa batun baya rasa nasaba da kokarin kasar na hadewa da kungiyar tsaro na Neto
Wannan sanarwar tazo ne kwana daya bayan da shugaban kasa Sauli Ninisto da kuma fira ministan a kasar Sanna Marin suka bayyana aniyar kasar na hadewar da kungiyar tsaro ta Nato ba da bata lokaci ba.
Kasar rasha ta yi gargadin cewa shigar kasar Finland cikin kungiyar tsaro ta Nato babbar barazana ce gareta , inda ministan harkokin tsaron kasar rasha ya matakin zai tilasatawa Mosko daukar mataken da suka dace da suka shafi dabarun soji don magance wannan abin da take gani a amatsayin barazana
Kasar rasha tana makwabtaka da kasashe 14 5 daga cikinsu mamabobi ne a kungiayr tsaro ta nato su ne Latvia, Estonia, Lithuania, Poland, da kuma Norway.