Kasar Rasha Ta Kwace Iko Da Fiye Da Rabin Muhimman Birane A Gabashin Ukrain.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar rasha sun kwace iko da muhimmancin biranen masana’antu dake gabashin kasar Ukrain a ci gaba da kokarin da suke yi na dannawa cikin yankin Donbas.
Anasa bangaren gwamnan yankin Luhansk Sergiy Gaiday ya fadi cikin wata samara day a fitar ta yanar gizo cewa halin da ake ciki a Severontsk yana da matukar sarkakiya , domin har yanzu sojojin na Uktanin na ci gaba da rike da ikon wasu yankuna a wajen
Daga lokacin da kasar Rasha ta kaddamar da harin soji kan kasar Ukrain a watan Fabarerun day a gabata, kasar Amurka da kawayenta sun aike da muggan makamai zuwa kasar Ukrain da kuma musayar bayanan sirri da gwamnatin kasa , agefe guda kuma suna kara kakaba takunkumi kan kasar rasha da sauran jami’an gwamnatinta.
READ MORE : Sojojin HKI Sun Harbe Wata Bafalasdinya Gabar Yammacin Kogin Jodan A Da Safe.
Ko a baya bayan nan ma shugabannin kasashen kungiyar tarayyar turai sun amince da yanke kashi 90% na dukkan man da take shigowa dashi daka kasar rasha zuwa yankin nan da karshen wannan shekarar da muke ciki.
READ MORE : Raisi; Iran Babbar Amintacciyar Abokiyar Tarayyar Nahiyar Africa Ce.