Kasar Rasha ta Dakatar Da Fitar Da Iskar Gas zuwa kasashen Turai.
Tun bayan da kasar Rasha ta kaddamar da yaki kan kasar Ukrain kasashen turai suka kakaba mata manyan takunkumai kan kamfanoni samar da makamashi na kasar, matakin da ya jefa kasasshen turai cikin mummunar matsalar makamashi,
Wanna yasa nan take kasar rasha ta dakatar da gas din da take fitarwa ta bututun Nord Strem 1 da hakan ya kara tsananta matsalar karacin makamashi a lokacin bazaar, a jiya juma’a kuma kamfanin samar da makamashi na Giant Gazprom na kasar rasha ya sanar da dakatar da aikewa da iskar gasa ta bututun da aka tsara saboda wata tangarda da aka samu har sai an kammala gyare-gyare.
Wannan mataki yazo ne yan sao’I bayan kasashen G7 suka ce suna ci gaba da shirye shirye na sanya takunkumi kan yawan farashin manfetur da kasar rash eke fitarwa , a wani yunkuri na rage yawan kudaden shigar da kasar Rasha ke samu da zata iya amfani da shi wajen ci gaba da mamaye kasar Ukrain.
Kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov da yke mayar da martani game da kokarin da kasashen turai ke yi na tsayar da farashi daya ga man fetur din kasar yace shirin kasashen na G7 zai kara dagular farashin mai ne a kasuwarsa ta duniya.