Kasar Rash Ta Zargi Amurka Da Aikewa Da Yan Ta’adda Daga Siriya Zuwa Kasar Ukrain.
Wani babban jami’in leken Asirin kasar Rasha ya bayyana cewa anan horasa da yayan kungiyar Ta’adda ta Daesh a sansanin sojojin Amurka dake Al tanf na kasar Siriya domin kwashe su zuwa kasar UKrain,
Bayanin ya ci gaba da cewa a karshen shekara ta 2021 wasu Amurka da aka sakosu daga gidan yari da yayan kungiayr ta’adda ta Daesh cikin hard a yan asalin kasar Rasha an kaisu sansanin sojojin kasar Rasha dake Al- tanf inda suke samun horo na musamman da dabarun yaki na yan ta’adda da zammar aikewa da su zuwa yankin Donbass.
Babban jami’an ya kara da cewa mafiyawancin yayan kungiyar yan ta’adda ta Daesh da aka aikasu zuwa kasar Ukrain an kashe su a lokacin farmakin da kasar rasha ta kai Ukrain, sai dai har yanzu Amurka tana kokari sake farfado da wata sabuwar cibiyar kungiyar ta Daesh a yankin gabas ta tsakiya da gabashin Afrika domin aikewa da su zuwa kasar Ukrain ta hanyar kasar Poland.