Kasar Pakistan Ta Zabi Sabon Shugaban Majalisar Dokoki.
Sabuwar kawancen Jam’iyu a majalisar ta zamo mafi rinjaye bayan da aka sanar da nadin tsohon fira ministan kasar Raja Pervaiz a matsayin sabon shugaban dokokin kasar. A jiya Asabar ne aka zabi tsohon fira ministan kasar dan shekaru 71 wato Raja Pervaiz Asharaf ba tare da hamayya ba da ya fito daga jam’iyar PPP a matsayin sabon shugaban majalisar dokokin kasar,na 22.
A farkon makon nan ne baya dogon lokacin da aka kwashe ana rikici kan kundin tsarin mulkin kasar daga karshe majalisar ta zabi shehbaz sharif dan shekaru 70 a matsayin sabon fira ministan kasar wanda ake kallonsa a amatsayin wanda yafi sanin makamar aiki sabanin siyasa, bayan da aka sauke gwamnatin Imran Khan na jam’iyar PTI.
Shi dai sabon shugaban majalisar shi ne dan takara daya tilo da babu wanda ya kalubalanceshi ya godewa shugaban jam’iyar sa da ya ba shi wannan damar ta ganin ya samu wannan mukami. Ashraf ya taba zama fira ministan kasar a shekara ta 2012 zuwa ta 2013.
Tun a ranar lahadi da ta gabata ce dubban magoya bayan tsohon Fira ministan kasar Imran Khan suka cika titunan kasar don gudanar da zang-zangar nuna adawa da abin da suka kira gwamnatin da aka shiga da ita daga waje.