Kasar Oman Na Goyon Bayan Iran Kan Halattaccen Hakkinta Na Neman A Cire Mata TaKunkumi.
Ministan harkokin waje na kasar Oman Sayyid Badr bin Hamad bin Hamood Al-Busaidi a wata zantawa ta wayar tarho da yayi da takwaransa na kasar Iran Amir Abdollahiyan ya fadi cewa mun yi amanna cewa dukkan bangarorin suna so a cimma yarjejeniya ta karshe kuma an samar da kyakkyawar daman a ganin an afkuwar hakan.
Yace a kowanne lokacin kasar Oman tana goyon bayan ganin an cimma yejejeniyar ta karshe a tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliya iran da kuma ganin an biya mata dukkan hakkokinta,
Anasa banagren minisatan harkokin wajen iran Amir Abdallahiyan ya jaddada cewa cin ma yarjejeniya ta karshe ya doru ne kan muhimman abubuwan guda biyu da suka hada da gaskiya da sassauto war Amurka kan ra’ayinta, kuma iran sa gaske take yi wajen ganin an cimma tabbataciyar yarjejeniya mai dorewa,
READ MORE : Mabiya Malam Zakzaky Sun Sha Alwashin Juyin Juya Hali A Najeriy.
Ya kara da cewa iran tana mayar da hankali sosai kan muhimmancin samar da makamashi da abinci a duniya kuma ya zuwa yanzu ta gabatar da shiye-shirye daban –daban bisa la’akari da kalubalen da duniya ke fuskanta game da abin da ya shafi makamashi.