Kasar Mali Ta Karbi Jiragen Yaki Na Soji Guda Biyu Daga Kasar Rasha.
Gwamnatin sojin kasar mali ta sanar da karba wasu sabbin kayayyakin aiki soji daga kasar rasha ga jami’an tsaron kasar, ciki har da jiragen yaki na soja guda biyu da kuma garkuwar kakkabo jiragen sama,
Bayanan da suka fito daga babban darakatann yada labarai da hulda da jama’a na jamia’an sojin kasar mali ya fadi cewa mun karbi karo na biyu na kayayyakin soji daga kasar Rasha wanda hakan ke tabbatar da kyakkyawar alaka mai amfani tsakaninsu da kasar ta rasha
Shugaban kasar Mali daya kwace mulki da karfin tsiya a watan Agustan shekara ta 2020 a tsakiyar tsanantar harkokin tsaro a kasar ya kara kusantar kasar Rasha ne baya day a raba gari da kasar Faransa, bayan da ta sanar da janye sojojinta da ta aike da su zuwa kasar ta mali,
A ranar 31 ga watan maris Bamako ya kaRBI Jiragen yaki na Soji guda biyu da garkuwar kakkabo makamai daga hannun rasha ,wasu bayanai sun bayyana cewa wadannan kayayyakin suna daga cikin abubuwa da aka kulla yarjejeniya ne tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a shekara ta 2019 na sayan jiragen sama masu saukar Ungulu guda bisa tsarin kudi da yafi jan hankali idan aka kwatanta da wanda kasashen turai suka bada.