Kasar Kuwait Ta Nada Sabon Jakadanta Na Farko A Kasar Iran Bayan Shekaru Shida.
Rahotanni sun bayyana cewa Kasar Kuwait Ta sanar da Nadin sabon Jakadanta na farko a kasar Iran bayan kwashe shekaru 6 da kasashen dame mambobi a kungiyar tekun fasha sun janye jakadunsau a kasar don nuna goyon bayan kasar Saudiya game da matakin da ta dauka na yanke dangantakarta da kasar Iran.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdollahian ya karbe takardun diplomasiya din Badar Abdullah Al-Munaikh a matsayin sabon jakadan kasar Kuwait a birnin Tehran , yayin da ita ma kasar Iran ta ayyana Mohammad Irani a matsayin sabon jakadanta a kasar Kuwait. Kuma dukkan bangarorin biyu suna kokari wajen bin hanyoyin da za’a kara kyautata dangantakar dake tsakaninsu
Wannan yana zuwa ne yan kwanaki bayan da minsitan harkokin wajen kasar Iran Amir- Abdollahiyan ya sanar cewa nan bad a jimawa ba kasashen Kuwait da hadaddiyar daular larabawa zasu aike da sabbin jakadunsu zuwa birnin Tehran.
READ MORE : MDD Da Rasha Sun Tattauna Game Da Cibiyar Nukiliyar Zaporijjia.
Kasar Kuwait ta raga kardin hulda diplomasiyyarta ne zuwa mtakin mai kula da manufofin kasar a Tehran a watan janerun shekara ta 2016.
READ MORE : Kenya; Wasu Mambobin Hukumar Zabe Sun Ce An Yi Magudi.