Kasar Kuwait Ta Bukaci A Kori Isra’ila Daga Kungiyar Tarayyar Majalisun Dokoki.
Kakakin majalisar dokokin kasar Kuwait ya soki irin manufofin siyasa mai harshen damo da hukumomin kasa da kasa ke nunawa kan gwamnatin yahudawan sahyuniya tare da yin kira da a kori wakilin na Isra’ila daga kungiyar tarayyar majalisar dokoki ta duniya,
Marzouk Ghanim ya fadi haka ne a wajen taron mambobin kungiyar majalisun dokokin da aka yi a jiya Asabar a kasar Indonesiya , inda ya kara da cewa gwamnatin Kuwait tana yin tir da duk wani nau’I na mamaya domin ita ma an yi mata mamaya shekaru 30 da suka gabata don haka tana adawa da duk wani nau’I na mamaya.
Yace: “ me yasa za’a bukaci a kori wakilan kasar Rasha daga cikin kungiyar alhali ta kaddamar da yaki kan kasar Ukrain ne a yan kwanaki da suka gabata, yayin da shekaru 60 ke nan gwamnatin yahudawan sahyuniya tana mamaye da yankunan falasdinawa amma ba’a bukaci a kori wakilanta daga cikin kungiyar ba.
Sai dai duk da yake cewa wasu daga cikin kasashen larabawa sun amince da daidaita hulda da Isra’ila amma dai kasar Kuwait ta bayyana adawarta a fili da daidaita duk wata hulda da gwamnatin mamaya ta Isra’ila.
Daga karshe ya nuna goyon bayan kasarsa a hukumance na kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kai da kuma nuna adawa da duk wani shirin daidaita hulda da Isra’ila