A ranar Juma’ar da ta gabata ce sojojin kasar Jamus suka fice daga wani sansanin sojin sama a Jamhuriyar Nijar da ke yammacin Afirka tare da jigilar dakarunsu na karshe zuwa gida, inda suka kammala janyewa daga yankin Sahel mai fama da rikici.
A karshen watan Mayu, Jamus da Nijar sun cimma yarjejeniyar wucin gadi da ta baiwa sojojin Jamus damar ci gaba da gudanar da aikin sansaninsu na jiragen sama a Yamai babban birnin kasar har zuwa karshen watan Agusta.
Amma tattaunawar tsawaita waccan yarjejeniya ta wargaje, musamman saboda ma’aikatan sansanin ba za su ci gajiyar kariya daga tuhuma ba.
Manyan jami’an sojin Jamus da na Nijar sun karanta sanarwar hadin gwiwa da ke bayyana kammala janye sojojin.
“Wannan janyewar ba zai kawo karshen hadin gwiwar soji tsakanin Nijar da Jamus ba, hasali ma bangarorin biyu sun kuduri aniyar ci gaba da kulla huldar soji,” in ji su.
Jiragen daukar kaya guda biyar dauke da sojojin Jamus 60 da tan 146 na kayan aiki sun sauka a sansanin sojin sama na Wunsdorf da misalin karfe 6:30 na yamma agogon kasar Sin wato (1630 GMT), inda sakataren tsaron kasar Nils Hilmer ya gana da su.
Tun a watan Fabrairun 2016 ne Jamus ke gudanar da sansanin a Nijar kuma ta taba daukar ma’aikata kusan 3,200.
Gwamnatin mulkin soja ce ke tafiyar da Jamhuriyar Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yulin shekarar 2023 da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ke tsare da shi tun daga lokacin.
Gwamnatin dai ta juya wa sauran kawayen kasashen yammacin duniya irinsu Faransa da Amurka baya da su koma ga Rasha da Iran.
Duba nan: Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da dala miliyan 100 domin…
An samu irin wannan sauyi a makwabciyar kasar Mali da Burkina Faso, wadanda su ma shugabannin sojoji ke mulka kuma suke fuskantar tashin hankali daga kungiyoyin masu jihadi.
A ranar 7 ga watan Agusta, Nijar ta sanar da yanke huldar diflomasiyya da Ukraine, bayan da ta yanke irin wannan hukunci a makwabciyarta Mali mai goyon bayan Rasha, bayan da ‘yan tawayen kasar suka yi artabu da sojojin Mali da sojojin haya na Wagner na Rasha a karshen watan Yuli, lamarin da Kyiv ya nuna cewa yana da hannu a ciki.
Daga baya kungiyar ‘yan tawayen da ta dauki alhakin fadan ta fitar da sanarwa inda ta musanta ikirarin taimakon kasashen waje.
Duba nan: Germany Ends Military Operations in Pro-Russian, Junta-Run Niger