Kasar Ivory Coast Ta Yi Kira Ga Mali Da Ta Gaggauta Sakin Sojojinta 49 Da Ta Kama.
Gwamnatin Ivory Coast ta bukaci kasar mali da ta saki dukkan sojojinta guda 49 da ta kama a ranar lahadi da ta gabata a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa dake Bamako ba tare da ba ta lokaci ba, kana ta yi watsi da zargin da ta yi na cewa sojojin haya ne
Har ila yau gwamnatin ta kara da cewa sojojin suna cikin dakarun sojin kasar ne, kuma sun isa kasar Mali ne domin gudanar da ayyukan tabbatar da zaman lafiya karkashin rundunar wanzar da zamana lafiya ta majalisar dinkin duniya .
Tun da fari dai kakakin gwamnatin kasar Mali kanar Abdullahi Mega ya zargi sojojin da shiga kasar ba bisa ka’ida ba da mallakar makaman yaki ba tare da izini ko umar ni wani ba.
READ MORE : Hamas; Kulla hulda Tsakanin Saudiyya da Isra’ila Cin Amanar Falasdinawa Ne.
A nasa bangaren mataimakin kakakin Majalisar dinkin duniya Farhan Haq yace rundunar ba ta bangaren rundunawar wanzar da zaman lafiya ta mali ba ce. ta kasashen da suke bada gudunmawar sojojin ne da suka taru domin talafawa dakarunsu, kuma wannan ba sabon abu ba ne a ayyukan wanzar da zaman lafiya.