Kasar Iran Za ta Fara Hako Man Fetur A Rijiyoyin Da Suke Hadaka Da Kasar Saudiya.
Ma’aikatar man fetur na kasar Iran ta bayyana cewa za’a bada zangon farko na kwangilar fara ayyukan hako mai a rijiyar mai ta Esfandiyar dake cikin teku, wadda ke hade da rijiyar mai ta Lulu ta kasar Saudiya.
Alireza Mahdizaeh wanda ke jagorantar kamfanin main a cikin teku na kasar Iran ya bayyana cewa za’a fara aikin hakar mai da kuma hako rijiyoyi guda hudu a kashin farko na ayyukan raya kasa a garin Esfandiyar mai nisan kilomita 95 daga kudu masu yammacin tsibirin kharg na iran ind aka kiyasta samun sama da gangar mai miliyan 500.
Har ila yau ya kara da cewa iran ta tattara albarkatunta na cikin gida domin bunakasa rijiyoyin mai da ke da iyaka da kasashe makwabta bayan takunkumin da Amurka ta kakaba mata a bangaren manfetur da ya hana kamfanoni kasashen waje zuwa jari a manyan ayyukan iskar Gasa da man Fetur
Daga karshe ma’aikatar ta sanar a watan maris cewa za ta fara fitar da iskar gas a rijiyoyin da suka yi Hadaka da kasashen saudiya da Kuwait bayan da kasashen larabawan guda biyu suka cimma matsaya na fara gina rijiyoyin.