Kasar Iran Na Adawa Da Daukar Matakin Soji Ko Yin Amfani Da Karfi Kan Wata Kasa A Yankin.
Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Said Khatib zade ya bayyana cewa kasar iran tana adawa da duk yin amfani da mataki suji ko kuma karfi kan wata kasa da zimmar warware wani rikici dake tsakaninsu, kuma tana daukarsa a matsayin keta hurumin da cin mutunci tsarin mulkin kasashen.
Wannan yana zuwa ne bayan da shugaban kasar Turkiya Dayyib rajab Ardogan yayi barazanar kaddamar da harin soji a kasar Siriya da nufin samar da tsaro a iyakar kasar ta kudu dake makwabtaka da kasar siriya.
Yace yin amfani da karfi zai kara dagula al’amura ne kawai, da kuma kara ruruta wutar fitinar da je dan adam cikin mummunan bala’I a yankin, yana mai cewa kaar iran ta fahimce damuwar da Turkiya take da shi kan batun tsaro, sai dai tattaunawa ce hanyar da ta fi dacewa wajen warware matsalar, da kuma mutunta kyakkyawar alakar dake tsakani musamman yarjejeniyar zaman lafiya ta Astana da aka kulla na kawo karshen rikicin kasar siriya.
Kasar siriya ta yi tir da kiran da shugaban kasar Turkiya yayi na kafa wani yanki mai Aminci a wani yankin arewacin kasar larabawa da aka mamaye.