Kasar Iran Ce Kan Gaba A Fagen Yaki Da Muggan Kwayoyi A Duniya.
Ministan harkokin cikin gidan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Kasar Iran ce ta yi fice a fagen yaki da muggan kwayoyi a duniya
A jawabinsa a ranar bikin yaki da muggan kwayoyi a duniya a cibiyar yaki da muggan kwayoyin da ke kasar Iran: Ministan harkokin cikin gidan kasar Iran Ahmad Wahidi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musuluncio ta Iran ta yi fice a fagen yaki da muggan kwayoyi musamman dakile gungun masu safarar kwayoyin daga wasu kasashe da suke ratsawa ta cikin kasar Iran domin isar da su zuwa sassan duniya.
READ MORE : Sojojin Amurka da na Birtaniya sun shiga tashar ruwan Nastoun na kasar Yamen.
Wahidi ya jaddada cewa: Yaduwar muggan kwayoyi tana daga cikin manya-manyan matsalolin duniya, don haka ya zame dole a kan kasashe su hada karfi da karfe wajen ganin sun kawo karshen wannan masifa a fagen rayuwar dan Adam.
READ MOER : Dole Burtaniya Ta Shirya Yaki Da Rasha – Sojin Burtaniya.
READ MORE : Rivers : Kotu ta ba da Belin Ɗan Majalisar tarayya bayan shafe kwanaki 62 a tsare.
READ MORE : Kotu ta yi watsi da batun ba da belin shugaban IPOB Nnamdi Kanu.