Le Drian yace yau ran shi a bace yake dangane da abinda aka yiwa kasar, domin bai dace ace kasashen dake kawance da juna suna yiwa junan su haka ba.
Ministan ya bayyana matakin a matsayin irin na lokacin shugabancin shugaba Donald Trump, lokacin da ya jagoranci Amurka yake kuma kama karya akan kawayen ta.
A wani labarin na daban hugaban Amurka Joe Biden ya bayyana kulla sabuwar yarjejeniyar ginawa Australia jiragen yakin karkashin ruwan bayan sanar da wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Birtaniya da kuma Australia, abinda zai baiwa Canberra damar mallakar tarin jiragen yakin karkashin ruwa masu amfani da nukiliya wadda Amurka ke sayarwa kawayen ta kawai.
Ministar tsaron Faransa Florence Parly ta bayyana matakin da Australia ta dauka a matsayin rashin tsayar da magana guda, yayin da ta kara da cewa Faransa ta fahimci yadda Amurka ke kula da kawayen ta.
Kamfanin dillancin labaran alfurat News ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Usman alghanimi ya bayyana cewa, a halin yanzu jami’an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba’in nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami’an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.
Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la’akari da matsalolin da aka rika samu a lokutan baya na hare-haren ‘yan ta’adda lokacin tarukan addini a kasar.
Yanzu haka dai jama’a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba’in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki.