Gwamnatin Kasar Chadi ta kafa dokar kar-ta-kwana akan karancin abinci a kasar, inda ta bukaci kasashen duniya da su kai mata dauki domin shawo kan matsalar.Wannan bukata na zuwa ne kwana guda kafin ganawar da za’ayi tsakanin shugaban kungiyar kasashen Afirka, Macky Sall tare da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow dangane da bukatar fitar da abinci daga Ukraine
Sanarwar tace gwamnati tayi kira ga masu bada agaji da kawayen ta na duniya da su taimaka wajen kai dauki ga jama’ar kasar da suke fuskantar karancin abincin.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar mutane miliyan 5 da rabi ke fuskantar karancin abinci a kasar ta Chadi, alkaluman dake nuna sama da kashi daya bisa 3 na jama’ar kasar, kuma suna bukatar daukin gaggawa.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a watan Maris da ya gabata tace akalla mutane miliyan 2 da dubu 100 ke bukatar taimakon abinci na gaggawa a Chadi a wannan wata na Yuni.