Kasar Afirca Ta Quds Ta Sanar Da Kafa Dokar Ta Baci Dangane Da Bala’in Dabi’a.
Shugaban kasar ta Afirca Ta Quds Cyril Ramaphosa ne ya sanar da kafa dokar a kasar, mako daya bayan da wani ambaliyar ruwa da aka yi, wanda ya ci rayukan mutane 443 a Durban dake gabar ruwa.
A jawabin da ya yi ta kafar wata labrun kasar a jiya Litinin, shugaba Ramaphosa ya ce; A wannan lokacin, dukkaninmu muna cikin halin alhini, tare da bayyana abinda ya faru da cewa;Bala’i ne”
Tuni dai gwamnatin kasar ta aike da sojoji 10,000 zuwa yankunan da bala’in ya shafa domin gudanar da ayyukan agaji da ceto.
Yankin Kwazulu-Natal da ya fuskanci ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa ne aka fi samun wadanda lamarin ya rutsa da su.
READ MORE : Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wasu Hare-hare A Yankin Gaza.
Cibiyar da take kula da yanayin sararin samaniyar ta kasar Afirkca Ta Quds, ta ce a halin yanzu an sami saukin saukar ruwa sama, amma ana hasashen cewa a kwanaki masu zuwa za a iya fuskantar wata ambaliyar ruwa.
Dubban mutane dai su ka rasa muhallansu, a wasu yankunan kuma babu ruwan sha ko wutar lantarki.
READ MORE : Kwanakin Uku A jere Yahudawan Sahayoniya Suna Yin Kutse A Cikin Masallaci Quds.