Kasashen Norwey, Biritaniya da kuma Amurka, da kuma kungiyar tarayyar turai (EU), sun yi tir da cafke ‘yan jagororin ‘yan adawa a Sudan.
A wata sanarwar bai daya da suka fitar bangarorin sun nuna damuwa game da kame kamen ‘yan adawan wanda suka ce ya yi hannun riga da alkawarin da sojojin dake rike da mulki a kasar suka dauka musamman na tattauna hanyoyin da zasu kai ga warware rikicin siyasar kasar.
Saidai mahukuntan na Khartoum, sun danganta kalamman na kasashen turan da Amurka da cewa tsoma baki ne dumu-dumu a cikin harkokin cikin gidan kasar.
A sanarwar da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan, ta ce furucin kasashen ya sabawa hanyoyin diflomatsiyya, saboda dukkan mutanen uku da ake tsare ana tuhumarsu ne da aikata laifuka.
Tun dai bayan juyun da akayi a watan Oktoba, daruruwa mutane ne aka cafke a kasar ta Sudan, sannan da dama sun mutu a zanga zangar kin jinin mulkin sojoji.