Bisa ga sakamakon zaben majalisar dokokin da aka gudanar a kasar Morocco a jiya Laraba, jam’iyyar RNI ta lashe kujeru fiye da sauran jam’iyyu a majalisar, biye da ita akwai jam’iyya PAM sannan jam’iyyar PJD ta masu kishin addinin ta sami kujeru 8 a majalisar, wannan shine sakamakon karon farko wanda jam’iyyar masu kishin addinin ta sha kaye.
Wannan dai shi ne sakamakon karon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar a kasar ta Morocco a ranar jiya Laraba.
Jam’iyar RNI wacce wani hamshakin attajiri kuma tsohon ministan noma na kasar, Aziz Akhannouch yake jagoranta ta sami kujeru 97 daga cikin kujeru 395 na majalisar dokokin kasar, biye da ita akwai Jam’iyyar PAM mai kujeru 82 daga nan sai jam’iyyar Istiqlal mai kujeru 78.
Jam’iyyar PJD dai ta sami kujeru 8 ne kacal bayan an kirga kashi 96% na kuri’un da aka kada.
A wani labarin na daban yau ne kwamitin da ke kula da shirya tarukan makon hadin kan musulmi na duniya ya fara gudanar da zamansa tare da halartar dukkanin mambobi.
Shugaban kwamitin Mahdi Agha Muhammad ne ya sanar da hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, inda ya bayyana cewa, zaman taron na farko da aka fara an tattauna yadda zaman zai kasance a wannan shekara.
A shekarar bara saboda matsalolin da ake ciki na bullar cutar korona, an gudanar da taron ne kai tsaye ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, inda masu gabatar da jawabai suka rika gabatar da jawansu da makaloli kai tsaye.
Ya ce har yanzu wanann batu yana daga cikin abin da yke ci wa al’ummomin duniya tuwo a kwarya, a kan haka sun fara tattaunawa kan yadda taron na bana ya kamata ya kasance, duk kuwa da cewa ba a yanke shawara guda kan hakan ba, amma za a ci gaba da tatatunawa domin samun matsaya guda.
Kwatin da ke daukar nauyin shirya tarukan hadin kan musulmi na duniya dai yana karkashin cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ne, da ke da babban ofishinta a birnin Tehran.
Marigayi Imam Khomenei ne ya kirkiro makon hadin kan musulmi musulmin duniya, wanda ya sanya makon haihuwar manzon Allah a cikin watan watan rabi’ul Awwal ya zama shi ne makon hadin kan musulmi na duniya baki daya.