Karon Farko, Blinken Da Lavrov, Sun Tattauna Tun Bayan Rikicin Ukraine.
A karon farko an yi tattaunawa tsakanin ministocin harkokin wajen Rasha da saktaren harkokin wajen Amurka, tun bayan rikicin Rasha da Ukraine.
A tattaunawar data wakana ta wayar tarho tsakanin Sergio Lavrov, da Antony Blinken, bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya shaidawa takwaransa na Rasha cewa duniya ba za ta taba amincewa ba da yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye.
‘’yana da kyau Rasha ta ji daga bakinmu cewa ba zamu taba amuncewa da ba da wannan, kuma hakan zai sa ne mu kara daukar mataki kan Moscow, a cewar Blinken.
A ansa bangare ministan harkokin wajen Rasha, Sergio Lavrov, ya kalubalanci matakin Amurka da NATO, na ci gaba da baiwa Ukraine makamai, wanda ya ce hakan zai kara tsawaita rikicin ne.
REA MORE : Lavrov; Kasashen Yammacin Duniya Na Adawa Da Ci Gaban Afirka.
Game da bukatar Amurka na ganin Rasha, ta mutunta yarjejeniyar da ta cimma da Ukraine a Turkiyya, kan fitar da hatsi kuwa, ministan harkokin wajen Rasha ya ce matakan da Amurka ta dauka kansa sun ne ke kara haifar da matsala wajen fitar da cimaka a kasashen duniya.