Karnataka Rikicin hana ɗalibai Musulmai sanya hijabi da ya birkita wata jihar Indiya.
Wata jiha a Indiya ta kulle manyan makarantun sakandare da manyan kwalejoji bayan da wani rikicin ya barke kuma ya ja hankalin duniya bayan da fitacciyar mai fafutukar kare hakkin mata kuma wadda aka ba lambar yabo ta Nobel Malala Yousufzai ta sanya baki.
Gwamnatin Jihar Karnataka da ke kudancin Indiya ce ta dauki matakin bayan zanga-zangar da dalibai suka yi kan hana mata Musulmi sanya hijabi a makaranta ya rikide zuwa na tashin hankali.
Ranar Laraba ake sa ran babbar kotun shari’a ta jihar za ta ci gaba da sauraran karar da aka kai gabanta wadda ake son ta tabbatar wa mata Musulmi damar da suke da ita ta sanya hijabi.
Wadannan lamurran sun auku ne bayan da wasu dalibai shida suka yi zanga-zanga a wata makarantar gwamnati da ta hana su sanya hijabi, zanga-zangar da ta bazu zuwa wasu makarantun.
Daga nan ne wasu dalibai mabiya addinin Hindu suka yi tasu zanga-zangar sanye da gyalulluka masu launin goro – launin da ake kallo a matsayin alamar mabiya addinin Hindu – wadda kuma suka yi domin nuna adawa ga sanya hijabin da mata Musulmi ke yi.
- Matar da ta koma namiji ta so kashe kanta saboda ana ƙyamarta
- Yadda al’ummar India ke alhinin mutuwar gawurtacciyar damisa mai ‘ya’ya 29
- An kama mutumin da ya kirkiri manhajar yin gwanjon mata Musulmai
A ranar Talata, shahararriyar mai fafutukar kare hakkin mata Malala Yousuzai – wadda shekarunta na haihuwa 15 yayin da ‘yan Taliban suka harbe ta saboda ta fito fili tana kare hakkin mata na samun ilimi a Pakistan – tayi kira ga shugabannin Indiya da su dauki matakin “hana muzgunawa mata Musulmi da ake yi”.
“Hana ‘yan mata halartar makaranta sanye da hijabinsu abin takaici ne,” inji Malala cikin wani sakon Twitter.
A Indiya wannan rikicin ya kara yawan fargaba tsakanin Musulmin jihar wadanda tsiraru ne, wadanda ke cewa tsarin mulkin kasar ya ba su damar sanya kayan da suke so.
Sai dai wani abu da ya ja hankali shi ne na yadda alkalin wata kotu ya yi kira ga daliban da sauran masu bayyana ra’ayinsu kan wannan batun da su “tabbatar da zaman lumana”.
Mene ne ummul haba’isin wannan rikicin?
Lamarin ya fara jan hankula ne bayan da wasu dalibai shida na wata babbar makarantar sakandare a gundumar Udupi ta jihar Karnataka suka fara zanga-zanga bayan da aka hana su shiga azuzuwansu saboda sun sanya hijabi.
Gundumar Udupi na cikin gundumomi uku na Karnataka da ke gabar teku – wanda kuma wuri ne da mabiya addinin Hindu ke da rinjaye sannan suna goyon bayan jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta firaminista Narendra Modi. Jam’iyyar BJP ce ke mulki a Karnataka.
Kwalejin ta ce ta kyale daliban su sanya hijbansu a cikin makarantar amma ta bukaci su cire su yayin da suke cikin azuzuzwa.
Sai dai masu zanga-zangar – wadanda dukkansu ke sanye da kayan makarantar da a hukumance aka amince da su – sun kafe cewa tilas a kyale su su rufe kawunansu yayin da suke cikin azuzuwa.
“Muna da malamai maza sai dai ba su da yawa. Muna bukatar rufe gashin kanmu a gaban maza. Wannan ne cikin dalilan da suka sa muke sanya hijabi,” inji Almas AH, daya daga cikin daliban yayin da ta ke hira da BBC Hindi.
Ba abin mamaki ne ba a ga mata sanye da hijabi da burka a Indiya, amma shugaban makarantar ya ce akwai bukatar malamai su rika ganin fuskokin daliban da suke koyarwa, kuma kayan makaranta na bai daya na tabbatar da ba a nuna wa dalibai bambanci ba.
Yadda rikicin ya bazu zuwa wasu makarantu
Batun sanya hijabi da mata Musulmi ke yi ya bayyana a wasu makarantun sakadare a Karnataka, amma ya fara jan hankali ne bayan da hotunan matan da ke zanga-zanga a Udupi suka yadu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta.
Ba da jimawa ba sai aka ga dalibai mata mabiya addinin Hindu na zuwa wasu makarantu sanye da gyalulluka masu lauyin ruwan goro – matakin da ya tilasta wa jami’an makarantun su hana su shiga makarantun su ma.
Daga nan ne gungun dalibai mabiya addinin Hindu- mazansu da matansu – suka rika yin maci domin nuna bacin ransu kan sanya hijabin da ‘yan uwansu dalibai Musulmi ke yi.
Sai dai ba a samu tashin hankali ba sai ranar Talata – sa’o’i kadan bayan da wata kotu ta fara sauraren karar da aka kai gabanta – inda rahotanni suka bayyana cewa an fara jefe-jefe da duwatsu a wasu birane.
A gundumar Mandya, wani bidiyon da ya bayyana ya nuna wata matashiya sanye da burka da wani gungun maza sanye da gyalulluka masu launin goro suka yi ma ta kawanya. Yayin da ‘yan Hindun ke ihu suna cewa Jai Shri Ram (jinjina ga ubangiji Ram), matar ta ki motsawa, kuma ta mayar musu da martani tana cewa “Allahu Akbar” (Allah ne mafi girma) yayin da jami’an makarantar kuma suke kokarin janye ta daga wurin.
Daga baya matar – wacce sunanta Muskan – ta ce shugaban makarantarta ya ba ta tabbaci cewa yana goyon bayanta.
Me gwamnatin jihar ta ce?
Ministan Ilimi na jihar Karnataka, Nagesh BC ya goyin bayan jami’an makarantun da suka hana sanya gyalullukan ‘yan Hindu da kuma hijabi a makarantun jihar.
Babban ministan jihar (wanda ke da mukamin gwamna) Basavaraj S Bommai tare da ministan cikin gida na jihar sun yi kira ga daliban da sauran jama’a da su “zauna cikin aminci da lumana” da juna.
Abin da kotu ta ce kawo yanzu
An shigar da kara har sau biyu a madadin masu zanga-zangar.
Lauyansu ya shaida wa kotun cewa umarnin gwamnatin jihar na hana daliban sanya hijabi ya taka tsarin mulkin Indiya – ya kuma bukaci kotun ta bayar da umarni na wucin gadi da zai ba daliban damar ci gaba da zuwa makaranta gabanin rubuta jarabawar da ke tafe.
Alkali Krishna Dixit ya ce zai dauki mataki daidai da abin da tsarin mulki ya tanada.
“Zan yanke hukunci daidai da rantsuwar da na sha. Wannan lamarin ba mai dadin ji ba ne, a ce an hana dalibai shiga azuzuzwa”, inji Alkali Dixit.