Kungiyar Kauracewa Isra’ila Movement (BDS) ta shirya wani shiri na musamman da za’a gudanar da kamfen a daidai lokacin da gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na ABNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hespers cewa, a yayin gasar cin kofin duniya da kasar Qatar ke karbar bakunci, kungiyar ta kauracewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da daukar matakan da suka dace da nufin inganta al’amuran Palastinu da kuma adawa da daidaita alaka da ‘yan mamaya na Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce: “A yayin gasar cin kofin duniya ta maza a Qatar da kuma yayin da miliyoyin mutane ke taruwa don tallafawa kungiyoyin da suka fi so, bari mu yi amfani da damar wajen kamfen na wayar da kan al’ummar Palasdinu da kuma ci gaba da fafutukar neman yancin kai. “Bari mu kara kokarin da muke yi na ganin an daidaita alaka da makiya Isra’ila tare da dakile duk wani yunkurin da wannan gwamnatin ke yi na dora kanta a matsayin wata kasa a yankin da kuma tsakanin kasashen Larabawa.”
A cikin bayanin wannan yunkuri, an bayyana cewa gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Qatar wata dama ce ta kauracewa tsarin da ya ginu bisa matsuguni da wariyar launin fata na Isra’ila, tare da kaurace wa duk wani kamfani da kungiyoyin da ke da alaka da wannan gwamnati ko kuma masu goyon bayanta.
Source:ABNA