Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza
Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza tare da bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin wani abu mai muni.
A yayin wani jawabi da ta yi a Alabama na tunawa da shekaru 59 na “Lahadin da aka Zubar da Jini,” ranar da jami’an gwamnatin jihar suka kai wa masu zanga-zangar kare hakkin jama’a hari a gadar Edmund Pettus da ke Selma, Harris ta ce tsagaita wutar za ta bayar da damar fitar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma ba da damar shigar da taimakon da ake bukata a Gaza.
Ta ƙara da cewa, “Kuma idan aka yi la’akari da ɗimbin wahala a Gaza, dole ne a tsagaita wuta nan da nan na aƙalla makonni shida masu zuwa, kuma a halin yanzu wannan batu yana kan teburin tattaunawa.”
“Wannan zai ba mu damar gina wani abu mai ɗorewa don tabbatar da cewa Isra’ila ta kasance cikin tsaro da kuma mutunta ƴancin al’ummar Falasɗinu na mutunci da ƴanci na cin gashin kai,” in ji ta.
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasɗinawa 127 A Wajen Karɓar Fulawa A Gaza
A baya-bayan nan ne sojojin Isra’ila suka kashe Falasɗinawa sama da 127 tare da jikkata sama da 760 a cikin kwanaki biyu kacal ta hanyar kai hari kan fararen-hula da ke ƙoƙarin karɓar agajin jinƙai, duk da cewa kotun duniya ta ICJ ta umarci Isra’ila da ta inganta yanayin jinƙai a Gaza.
Ko da yake a ranar Alhamis ɗin da ta gabata sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan taron Falasɗinawa da ke jiran manyan motocin dakon kaya a unguwar Al Nabulsi da ke Kudancin Gaza.
Kotun ta ICJ ta yanke hukunci kan taƙaddamar da ke tsakanin jihohi kuma umarninta na da nasaba da doka, amma ba ta da hanyar tabbatar da aiwatar da hukunce-hukuncenta.
Duba Nan: Bayan Fara Yakin Gaza Shin Me Ke Faruwa?
Sojojin Isra’ila sun yi iƙirarin cewa mutanen ne suka tunkari sojojinsu, lamarin da suke ganin zai jefa su cikin haɗari, don haka suka mayar da martani ta hanyar buɗe wuta.