Kakakin Majalisar Iran Da Shugaban Tajkistan Sun Jaddada Muhimmancin Bunkasa Alaka Tsakani.
A lokacin ganawarasa da shugaban kasar Tajikistan Emomali Rahmon , kakakin majalisar dokokin kasar iran Mohammad Bagher Ghalibaf, ya fadi cewa danganataka tsakanin kasashen biyu ta kara bunkasa sosai a yan watanni baya bayan nan, amma bat a kai matsayin da ake bubata ba.
Haka zalika ya nuna fatansa na ganin kasashen biyu sun bunkasa dangantakar tattalin arziki sake tsakaninsua nan gaba kadan, musamman ta hanyar karfafa bangaren kamfanoni masu zaman kansu
Anasa bangaren shugaban kasar ta Tajikistan yace Iran ta samu ci gaba sosai a shekarun baya bayan nan, ya kara cewa ci gaban da kasar iran ta samu a bangaren fasahar nukiliya ta zaman lafiya da kuma rashin tasirin takunkumin da aka kakaba mata ya nuna irin ci gaban da kasar ta samu, kuma a shirye muke mu yi aiki tare da kasar Iran a bangarori daban daban.
READ MORE : Masar Zata Sayarwa Kasar Poland Da Wasu Kasashen Turai Iskar Gas.
Shugaban kasar Tajikistan Emamo Ali Rahmon yana ziyara kwanaki biyu a kasar iran tare da babbar tawaga dake mara masa baya.
READ MORE : Sudan; An Saki Wasu ‘Yan Zanga-Zangar Da Aka Kama A Kasar Sudan A Jiya Litinin.