Shugaban Tunisia Kais Saied ya zargi wasu ‘yan siyasa da kitsawa kasar manakisa ta hanyar amfani da ‘yanciraninta da ke ketare musamman wadanda ke Faransa.
Kaise wanda bai kama suna wadanda ya ke zargi da kitsawa kasar manakisa ba, ya ce ‘yan siyasar kasar da ke ketare su na amfani da ‘yan ciranin Tunisa wajen caccakar manufofinta.
Kalaman na Kais Saied na matsayin shagube kan magabacinsa Moncef Marzouki da a baya-bayan nan ya bayyana salon kamun ludayinsa da yunkurin juyin mulki.
Ba tare da ambatar sunan Marzouki ba, shugaba Kais ya mayar da martini kan kalaman tsohon shugaban da yanzu ke Faransa da zama.
Marzouki wanda ya shugabancin Tunisia daga shekarar 2011 zuwa 2014 yayin wani jawabinsa gaban masu zanga-zangar adawa da Kais Saied a birnin Paris, ya bukaci Faransa ta yi fatali da duk wata bukata da Tunisa ta shigar mata ko kuma yunkurin taimakawa kasar kan abin da ya kira kama karya da kaucewa tsarin dimukradiyya da ke faruwa a kasar.
Sai dai shugaban na Tunisia wanda a farkon makon nan ya kafa majalisar bayan rusheta a baya, ya caccaki kalaman na Marzouki tare da bayyana shi a matsayin maci amanar kasa.