Kafofin yada labarai daban-daban na duniya sun mayar da hankali kan bukukuwan zagayowar lokacin juyin Iran a wannan shekara da juyin ya cika shekaru 43.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya rubuta a cikin wani rahoto cewa: “Sakamakon barkewar cutar Corona, a shekara ta biyu a jere, a cikin dubban motoci da babura ne muta ne suke yin bikin zagayowar ranakun juyin juya halin Iran a wannan shekara ma da juyin ya cika shekaru 43 miliyoyin mutane sun yi jerin gwano a ranar Juma’a.”
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, al’umma sun yi ta rera take guda a wannan a gabashi da yammaci da arewa da kuma kudancin kasar Iran, na nuna goyon baya tsarin jamhuriyar musulunci.
Tashar Faransa 24 kuwa ta bayar da labarin tattakin 22 Bahman ta hanyar buga rahoton bidiyo. Rahoton da kafar yada labarai ta fitar, dangane da halin da ake ciki na barkewar annobar korona, ya bayyana cewa a wannan tattakin na bana an yi shi ne da motoci da babura.
Bugu da kari, sojojin lema sun sauka kusa da dandalin Azadi kamar yadda aka saba, inda kuma aka rika jefa furanni daga jirage masu saukar ungulu ga masu jerin gwano.
Al-Mayadin ya kuma bayar da rahoto kan tattakin kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito, al’ummar Iran sun gudanar da bukukuwan cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar da kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya.