Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewar kafa kasar Falasdinu akan hanyar diflomasiya ce kawai zai tabbatar da makomar zaman lafiyar haramtacciyar kasar Isra’ila a Yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban yace yana da yakinin cewar samun kasashe biyu shine zai tabbatar da zaman lafiyar kasar Yahudawa ta isra’ila domin ci gaba da wanzuwar ta tare da kasar Falasdinu cikin ‘yancin dimokiradiya.
Biden yace amma akwai duguwar tafiya kafin cimma wannan buti, duk da yake ba zasu yanke kauna ba wajen fatar ganin an samu ci gaba.
Wannan matsayi na shugaba Biden ya nuna sauyin matsayin Amurka bayan saukar shugaba Donald Trump daga karagar mulki wanda gwamnatin sa taki goyan bayan kafa kasar Falasdinu, abinda ya sa shugabannin Falasdinawa suka ki tattaunawa da wakilan ta domin warware rikicin Gabas ta Tsakiya.
A kwanakin da suka gabata shugaba Biden ya karbi bakuncin Firaministan Isra’ila Naftali Bennet da kuma ministan tsaro Benny Gantz inda ya gana da su a lokuta daban daban.
A wani labarin na daban rundunar sojin saman Isra’ila tace, jiragen samanta sunyi luguden wuta wasu wurare biyu a Gaza a wannan Lahadin, bayan da mayakan yankin suka yi arangama da sojoji a kan iyaka tare da harba balambalan masu fashewa zuwa kudancin Isra’ila.
Sojojin Isra’ila sun ce “jiragen yakin sun kai hari kan sansanin sojan Hamas da ake amfani da shi wajen kera makamai da horo da kuma mashigin wani hanyar karkashin kasa da mayakan ke amfani da shi a kusa da Jabalia.
Sanarwar ta ce “Harin na mayar da martani ne ga kungiyar Hamas da ta harba balan-balan dauke wuta a yankin Isra’ila da kuma tarzomar da ta auku kafin lokacin.”
Sojojin sun ce duka abubuwan da suka faru “misalai ne na yadda Hamas ke ci gaba da amfani da dabarun ta’addanci da kai hari kan fararen hula.”
Babu wani rahoto daga Zirin Gaza na asarar rayuka sakamakon hare -haren na Isra’ila.
Da yake magana a Washington, inda ya gana da shugaban Amurka Joe Biden, Firayim Ministan Isra’ila Naftali Bennett ya ce ya dora wa Hamas da masu kishin Islama alhakin duk wani tashin hankali daga yankin Falasdinawa.