An kaddamar da babban taron na’urar mutum mutumi, na kasa da kasa na shekarar 2021 a nan birnin Beijing a jiya Juma’a, a sa’i daya kuma an kaddamar da bikin baje kolin na’urorin mutum mutumi na kasa da kasa na bana, inda kamfanoni sama da 100 suka nuna na’urori fiye da 500 da suka samar, wadanda suka hada na’urar mutum mutumi na masana’antu, da na ba da hidimomi, da jigilar da kayayyaki da kuma na’urar mutum mutumi na amfanin musamman.
Kawo yanzu wato bayan kokarin da kasar Sin take yi a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, ta riga ta ba da gudummowarta ga aikin raya sana’ar samar da na’urar mutum mutumi na kasa da kasa.
Yayin bikin kaddamar da babban taron na’urar mutum mutumin kasa da kasa na shekarar 2021 da aka shirya jiya, mataimakin ministan ma’aikatar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin Xin Guobin ya bayyana cewa, nan gaba kasarsa za ta kara mai da hankali kan aikin nazari da kuma samar da na’urorin mutum mutumi masu inganci.
Alkaluman da hadaddiyar kungiyar samar da na’urar mutum mutumi na kasa da kasa ta fitar sun nuna cewa, darajar sana’ar samar da na’urar mutum mutumi a fadin duniya ta karu daga dalar Amurka biliyan 20.4 a shekarar 2016 zuwa dalar Amurka biliyan 34.3 a shekarar 2020, darajar dake karuwa da kaso 13.9 bisa dari a ko wace shekara
A wani labarin na daban an kaddamar da dandalin taron hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu da dandalin taron raya rukunin masana’antu tsakanin kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, wanda zai gudana daga jiya zuwa yau, 11 ga wata a Nanning, fadar mulkin lardin Guangxi dake kudancin kasar Sin.
Yayin taron dandalin, an shirya bikin daddale kwangilolin ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, inda aka daddale kwangiloli 36 a zahiri da kuma kafar yanar gizo, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 20.
Babban taken dandalin shi ne “ingiza hadin gwiwa ta hanyar raya rukunin masana’antu bisa sabon tsarin samun ci gaba”, kuma makasudin shirya taron dandalin shi ne, sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa a bangaren samar da kayayyaki bisa shawarar ziri daya da hanya daya ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa, da kuma moriyar juna.