Tsohon Firaministan Guinea kuma jagoran ‘yan adawa, ya bukaci kungiyar ECOWAS da kada ta kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a makon da ya gabata, matakin da ya bayyana a matsayin ci gaba ga kasar ta su.
Sojojin da ke mulkin Guinea na fuskantar matsin lambar diflomasiyya bayan da dakaru na musamman karkashin jagoran cin Laftanar Kanal Mamady Doumbouya suka kwace mulki ranar Lahadin da ta gabata tare da cafke tsohon shugaba Alpha Conde.
A ranar Larabar da ta gabata ne kuma kungiyar ECOWAS ta dakatar da Guinea, yayin da a ranar Juma’a, kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bi sahu.
A wani labarin na daban tawagar kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afirka ta isa Guinea domin tattaunawa da shugabannin sojojin kasar da suka yi juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba Alpha Conde.
Sannu a hankali dai rayuwa a babban birnin kasar Conakry ta koma daidai a ranar Alhamis, inda aka sake bude kasuwanni, tare da ci gaban harkokin yau da kullum.
Laftanar Kanal Doumbouya na ci gaba da nanata cewa ya dauki matakin juyin mulki ne domin maslahar al’ummar Guinea, inda ya zargi gwamnatin Conde da cin hanci da rashawa da kuma take ‘yancin ‘yan kasa.
Doumbouya ya yi alkawarin kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadin kan kasa, sai dai bai fayyace lokaci da zai aiwatar da alkawarin ba.