Josep Borrell; Amsar Da Iran Ta Bayar Dangane Da Fardado Da JCPOA Abar Yabawa Ce.
Jami’i mai kula da al-amuran harkokin kasashen waje na tarayyar Turai Josept Borrell ya bayyana cewa amasar da gwamnatin Iran ta bayar dangane da farfado da yarjeniyar JCPOA tana da kyau kuma shaware ce wanda hankali zai amince da ita, don haka a halin yanzu muna jiran gwamnatin kasar Amurka bayyana matsayinta dangane da shawarorin na Iran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Borrell yana fadar haka a jiya litinin ya kuma kara da cewa tuni sun aikawa gwamnatin Amurka kofin amasar, kuma muna jiran amsarta a gwamnatnce. Borrell ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a a wata jami’a a arewacin kasar Espania.
A halin yaunzu watanni 16 ake ta tattaunawa da gwamnatin Amurka amma ta kungiyar tarayyar Turai don dawo da ita cikin yar Amurka cikin yarjeniyar ta JCPOA, da kuma dagewa Iran dukkan takunkuman zalunci wanda gwamnatin kasar Amurka ta dora mata bayan ficewarta daga yarjeniyar a shekara ta 2018.
Mohsen Naziri Asl, sabon jakadan Iran a cibiyoin MDD da ke Vienna ya gana da tokwaransa na kasar Rasha Mikhail Ulyanov, inda suka tattauna batun farfado da yarjeniyar, inda ya ce gwamnatin Amurka tana jan kafa wajen amincewa da dagewa iran takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata.