Rundunar sojin Isra’ila ta kama wasu Falasdinawa 60 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu, wanda ya kawo adadin Falasdinawa da aka tsare tun ranar 7 ga Oktoba zuwa 3,260.
An kama mutanen ne tsakanin daren Lahadi zuwa wayewar garin Litinin a garuruwan Bani Na’im da ke kusa da Hebron da Kafr Nima a cikin gundumar Ramallah da Jenin da Nablus, da kuma Baitalami, in ji sanarwar.
0904 GMT — Samar da kasashe biyu ya zama wajibi domin dakatar da rashin mutuncin Isra’ila — Jordan
Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya ce dole a soma aiki na tabbatar da kasashe biyu “domin kawo karshen wannan rashin imani” na Isra’ila.
Ya bayyana haka ne a wurin taro kan Hadin Kan Kasashen Yankin Tekun Bahar Rum da ke faruwa a Barcelona.
Ana sa rai wakilai arba’in da biyu za su halarci taron, galibinsu kuma wakilai daga ma’aikatun harkokin waje.
Shugaban tsare-tsaren kasashen waje na Tarayyar Turai, Josep Borrell da Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ne suke jagorantar taron.
isra’ila ba ta halarci taron ba, wanda a baya ya mayar da hankali kan hadin kai tsakanin Tarayyar Turai da Kasashen Larabawa.
0845 GMT — Hamas da Isra’ila na nuna damuwa kan sunayen fursunonin da za a yi musaya
Isra’ila da Hamas sun nuna damuwa kan jerin sunayen ‘yan Isra’ila da kuma Falasdinawan da za a saki a ranar Litinin, kamar yadda wani jami’in Qatar ya bayyana.
Jami’in ya ce masu shiga tsakani na kasar Qatar na aiki tare da Hamas da Isra’ila domin ganin sun shawo kan matsalar domin kauce wa jinkiri.
A kwanaki uku da suka gabata na yarjejeniyar tsagaita wutar, Isra’ila ta bayar da sunayen mata da matasan da za a saki daga gidan yari haka ita ma Hamas ta bayar da sunayen farar hular da za a saki dukansu sa’o’i 12 kafin lokacin sakin.
Ana kyautata zaton akwai yiwuwar a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas / Hoto: Reuters / Photo: AP
0100 GMT — ‘Yan kasar Thailand da aka saka daga Gaza suna cikin koshin – Firaiminista
Karin ‘yan kasar Thailanda guda uku da aka kungiyar Hamas ta saka daga Gaza suna cikin koshin lafiya, a cewar Firaiministan kasar Srettha Thavisin a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.
“Ina cike da farin ciki happy,” in ji Srettha, inda ya kara da cewa mutanen uku suna cikin koshin lafiya kuma ba sa bukatar kulawar gaggawa.
Kawo yanzu, an saki ‘yan kasar Thailand 17 daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su ranar bakwai ga watan Oktoba kuma yanzu za a mayar da su Thailand da zarar an samu sarari, a cewar wata sanarwar Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar.
0000 GMT — Hamas tana so a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila
Kungiyar Hamas da ke fafutukar kare mutuncin Falasdinawa ta sanar da cewa tana neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana hudu da ta kulla da Isra’ila a Gaza.
Wani Bafalasdine da aka saka ya hadu da ‘yan uwansa a Birnin Kudus ranar 27 ga watan Nuwamban 2023, a ci gaba da shirin musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra’ila / Hoto: Reuters
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce tana yin gagarumin yunkuri na ganin an saki karin Falasdinawa ko da bayan an kawo karshen yarjejeniyar ne.
Wani Bafalasdine da ke da masaniya kan wannan batu amma ba ya so a ambaci sunansa domin ba a ba shi damar magana da manema labarai ba ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Hamas ta shaida wa Qatar da Masar da ke shiga tsakani cewa a shirye take ta tsawaita yarjejeniyar da kwana biyu zuwa hudu.
A kwanaki uku na farkon yarjejeniyar, Hamas ta saki Isra’ilawa
40 da ‘yan kasashen waje 18, yayin da ita kuma Isra’ila ta saki Falasdinawa 117.
Source: TRThausa