Shugaban Amurka Joe Biden zai tattaunawa da Shugaban China Xi Jimping da nufin neman China ta kaucewa batun taimakawa Russia a wannan yaki da Rasha ke yi da Ukraine kusan kwanaki 23 da soma yakin.
A jiya alhamis joe biden ya ta fito karrara inda ta bayyana shirin sa na sanyawa China matsin lamba don ganin ba ta goyi bayan mammayar da Rasha ke yiwa Ukraine yanzu haka.
Shugabanin kasashen biyu za su tattaunawa ta wayar talho a yau juma’a,yayinda wasu rahotanni ke nuni cewa Amurka ta nuna matukar damuwa bayan samun labarin cewa China na kokarin taimakawa Rasha da makamai da za a yi amfani da su a Ukraine.
Wannan tattaunawa tsakanin Joe Biden da Xi Jimping ,tamkar kashedi ne Amurka ke yiwa China na cewa har ta kuskura ta taimawa Rasha a wannan yaki da take da Ukraine,China ba za ta ji da dadi ba, kamar dai yada shugaban diflomasiyar Amurka Anthony Blinken ya tseguntawa manema labarai.
Daddadiyar hulda dake tsakanin China da Rasha na fuskantar kalubale a cewar mashar’anta ganin ta yada manyan kasashen Duniya ke fatan ganin China ta juyawa Rasha baya,duk da haka China na mammaki karfi da Ukraine ke ci gaba da nunawa tun bayan barkewar wannan yaki .