Rahotanni daga Jihar Neja sun ce, yara kanana da shekarunsu suka kama daga 5 zuwa 12 sun rasa rayukansu, sakamakon harin da wani jirgin yakin Najeriya ya kai a yankin Kuregba da ke karamar hukumar Shiroro.
Sai dai wasu bayanai sun ce harin jirgin yakin Najeriyar ya fada kan fararen hula ne a bisa kuskure, a lokacin da sojin ke kokarin tarwatsa wata maboyar ‘yan ta’adda a wani yanki na karamar hukumar ta Shiroro.
Kakakin Gamayyar Kungiyoyin fararen hula a Shiroro Salis Mohammed Sabo, ya ce lamarin ya faru ne da safe a lokacin da yara ke diban ruwa a wata rijiyar burtsatse da ke unguwar Kurebe, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Zuwa lokacin wannan wallafa dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai kan faruwar al’amarin ba.
A cikin watan Satumban shekarar 2021, an taba samun irin wannan kuskure, inda wani jirgin yakin Najeriya ya kashe fararen hula ba tare da niyya ba a hare-haren da ya yi nufin kaiwa kan mayakan Boko Haram a arewacin jihar Yobe.
Mazauna kauyen Buhari da ke gundumar Yunusari a kusa da kan iyaka da Nijar, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu akalla 19 suka jikkata yayin hare-haren jiragin yakin.
A wani labarin na daban mambobin gwagwarmayar musulunci na najeriya sun dawo cigaba da jerin gwano a manyan biranen kasar domin kira ga gwamnatin muhammadu buhari ta saki takardun fasfo din jagoran ‘yan gwagwarmayar domin ya fita neman lafiya a kasashen katare sakamakon tabarbarewar lafiyar sheikh Ibrahim Zakzaky din.
Tun watannin baya dai kotu ta saki jagoran daga tsarewar fiye da shekara shidda da gwamnati ta masa amma an hana shi fasfo din sa dana mai dakin sa.