Jirgin Ruwan Birtaniyya Da Aka Kai Wa Hari A Tekun Bahar Maliya Na Dauke Ne Da Man Da Isra’ila Ke Anfani Da Shi Wajen Kai Hare-Haren Bam A Gazza
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya bayar da rahoto bisa nakaltowa daga kafar sadarwa ta Al-Mayadeen cewa, jirgin ruwan kasar Birtaniya da sojojin ruwan kasar Yamen suka kai wa hari a daren Juma’a yana dauke da man da gwamnatin sahyoniyawa ke amfani da shi wajen kai hare-haren bam a gazza.
Kamfanin dillancin labaran Abna-Al-Mayadeen ta rawaito cewa: Jirgin ruwan Birtaniya da sojojin ruwan Yaman suka kai wa hari a tekun Bahar Maliya yana kan hanyarsa ta zuwa yankunan da aka mamaye na Falasdinu ba hanyar Girka ba.”
Wadannan majiyoyi sun shaidawa Al-Mayadeen cewa jiragen ruwa na Amurka da na Birtaniya guda 2 ne suka raka wannan jirgin a kan hanyarsa ta ruwa don samar da kariya da kulawa, amma lokacin da sojojin Yaman suka matso kuma fadan ya barke, sai jiragen kariya guda biyu suka gudu suka bar jirgin Birtaniya dauke da mai shi kadai.
Majiyoyin siyasa sun shaidawa kafar yada labarai ta al-Mayadeen cewa, tserewar jiragen yakin Amurka da na Birtaniyya ya haifar da babbar tambaya ga masu neman tabbatar da tsaron yankin tare da kasancewar dakarun kasashen waje.
Kamfanin tsaron teku na Biritaniya “Ambury” ya sanar a safiyar yau a cikin sanarwar cewa wani jirgin ruwa na kasuwanci (jirgin dakon mai) wani makami mai linzami ya afka masa a kudu maso gabashin Aden a daren Juma’a kuma ya kama da wuta yana ci.
A gefe guda kuma, kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin kamfanin “Trafigura” na ruwa yana bada rahoton cewa, bayan harin da dakarun kasar Yemen suka kai kan jirgin ruwan dakon mai na kamfanin a tekun Bahar Maliya, daya daga cikin tankunan jirgin ya kone kurmus sannan kuma an yi amfani da na’urorin kashe gobara don sarrafawa da kuma shawo kan gobarar.
Source: ABNAHAUSA