Jirgin ruwa ɗauke da kusan tan 200 na abinci ya kama hanyar zuwa Gaza daga wata tashar ruwa ta Kudancin Cyprus, a wani yunƙuri na buɗe wata sabuwar hanya ta ruwa domin kai agaji ga jama’ar Gaza.
Jirgin ruwan na ƙungiyar agaji da ceto ta Open Arms an hange shi yana barin tashar ruwa ta Larnaca ɗauke da kusan tan 200 na shinkafa da fulawa da abincin gina jiki.
Wannan aikin kai agajin, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ke ɗaukar nauyinsa, inda ƙungiyar World Central Kitchen ke shiryawa sai kuma ƙungiyar agaji ta Proactiva Open Arms da ke ƙasar Sifaniya ke bayar da jirgin dakon kayan.
Maroko ta soma jefa wa jama’ar Gaza kayan agaji ta jirgin sama
Ƙasar Maroko ta shiga sahun wasu ƙasashen duniya domin kai kayan agaji Gaza inda a karon farko ita ma ta jefa wa jama’ar Gaza kayayyakin agaji ta jirgin sama.
Jaridar Hespress ta ruwaito wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Waje ta Isra’ila tana cewa gwamnatin Rabat ta buƙaci aika jiragen agaji zuwa Tel Aviv da arewacin Gaza.
Gwamnatin ta Morocco tare da haɗin gwiwar Isra’ila sun tura jirage shida ɗauke da kayan agaji.
Mayaƙan Houthi sun kai wa jirgin ruwan Amurka hari a Bahar Maliya
Mayaƙan Houthi sun kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka Bahar Maliya, kamar yadda mai magana da yawun ƴan Houthin Yahya Sarea ya tabbatar.
“Sojojin ruwan Yemen da taimakon Allah sun kai hari kan wani jirgin Amurka Pinocchio a Bahar Maliya da rokoki na ruwa da dama, kuma an samu jirgin yadda ya kamata, godiya ga Allah,” kamar yadda Sarea ya bayyana a wata sanarwa.
Sarea ya yi gargaɗi kan cewa ƙungiyar za ta ƙara zafafa ayyukan da take yi a cikin watan Ramadana “domin nuna goyon baya ga ƴan uwanmu kuma masu jihadi Falasɗinawa waɗanda ake zalunta.”
Duk da hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Birtaniya ke kai wa mayaƙan, mayaƙan na Houthi na ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan da ke hanyar zuwa Isra’ila ko kuma mallakar Isra’ilar.
Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen
Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da jikkata 14 a wasu hare-hare da aka kai a yammacin ƙasar Yemen, kamar yadda kakakin gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da shi ya sanar.
An kai hare-hare ta sama aƙalla sau 17 a kasar, ciki har da babban birnin Hudaida mai tashar jiragen ruwa da kuma tashar ruwa ta Ras Issa, a cewar Al Masirah, babbar kafar yaɗa labaran Houthi.
Duk da hare-haren da ƙawancen Amurka da Birtaniya ke kaiwa da kuma na wasu rundunonin sojin ruwa, Houthis sun zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa “mallakar Isra’ila ko mai zuwa Isra’ila” a ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya.
‘Yan Houthi sun ce za a ci gaba da kai hare-hare har sai Isra’ila ta dakatar da mamaye da kuma yaƙi a Gaza.
Biden ya ce bai shirya ganawa da Netanyahu ba
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce bai shirya ganawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ba.
DUBA NAN: Jeffery Shaun Dan Gwagwarmayar Amurka Ya Musulunta Saboda Falasdin
Biden ya kuma ce ba shi da wani shiri “a halin yanzu” na yin jawabi ga majalisar dokokin Isra’ila.