Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hare-hare A cikin Yankuna Mabanbanta Na Kasar Yemen.
Tashar talabijin din ‘almasirah’ ta kasar Yemen ta ambaci cewa; Tun a jiya da dare ne dai jiragen saman kasar na Saudiyya su ka fara kai hare-hare a cikin kasar ta Yemen a gundumar Hadhra-maut.Har ila yau, jiragen yakin sun kai wasu hare-haren a gundumar Zammar.
A jiya Juma’a ne dai kakakin sojan kasar Yemen, Janar Yahya Sari, ya sanar da cewa; sun kai hari a cikin yankuna daban-daban na Saudiyya da jiragen sama marasa matuki
Yankunan da hare-haren na sojojin Yamen su ka shafa sun hada, cibiyoyin man fetur na Aramco da filin jirgin sama na soja da ke garin Abha.
Kakakin sojan na Yamen ya kuma ce; Manufar wannan harin dai shi ne; Kokarin kawo karshen killace kasar Yemen da Saudiyya da kawayenta na yaki su ka yi.
Yakin da Saudiyya ta shelanta akan kasar Yemen ya shiga cikin shekara ta takwas, wanda ya zuwa yanzu ya haddasa asarar rayuka da dama da kuma jikkawa wasu dubun dubata.
READ MORE : Iran Tana Da Hakkin Mayar Da Martani Akan Ta’addancin HKI.