Jiragen yakin Isra’ila sun kashe daruruwan Falasdinawa sannan suka jikkata da dama a hare-haren da suka kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke Gaza da aka yi wa kawanya, a cewar jami’ai da kuma kafafen watsa labarai.
“Jiragen yakin Isra’ila sun yi luguden wuta a gidaje da dama da ke tsakiyar sansanin, lamarin da ya kai ga mutuwar akalla mutum 400, galibinsu kananan yara,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA ya rawaito.
Mutane da dama sun mutu sakamakon hare-haren, a cewar kakakin Ma’aikatar Cikin Gida ta Gaza Iyad al Bozom a wani taron manema labarai da ya gudanar, yana mai karawa da cewa jiragen yakin sun yi barin wuta a gidajen jama’a da ke sansanin kuma yawancin wadanda suka mutu mata da kananan yara ne.
Ya ce jiragen yakin Isra’ila sun ragargaza daukacin rukunin gidaje da aka fi sani da Block 6.
“Mutum fiye da 50 sun yi shahada kuma kimanin mutum 150 sun jikkata sannan gommai suna karkashin baraguzan gine-gine da suka danne su, a wannan hari na kisan kiyashi da aka kai a gidajen da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Zirin Gaza,” a cewar sanarwar da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar.
Ma’aikata a Asibitin Indonesia da ke Gaza sun Isra’ia ta kashe Falasdinawa sama da 500 sanna ta jikkata fiye da 150 yayin da jiragen yakinta suka yi feshin wuta da abubuwa masu fashewa a tsakiyar sansanin ‘yan gudun hijirar da ke arewacin Gaza.
Bidiyoyin da aka rika watsawa sun nuna gomman gawawwaki da aka zakulo daga baraguzan gine-gine. Mutane sun yi cirko-cirko yayin da wasu ke zakulo mutane daga wasu manyan ramuna da jiragen suka yi sakamakon harin.
Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila Laftanar Kanar Richard Hecht, ya tabbatar wa CNN cewa sun kai hari a sansanin Jabalia, yana mai cewa suna neman wani kwamandan kungiyar Hamas ne, ko da yake bai bayar da wata shaida kan hakan ba.
Source: TRT HAUSA