Jiragen Yakin HKI Sun Keta Hurumin Sararin Samaniyar Kasar Labanon.
Kudurin da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya fitar mai lamba 1701 bayan kawo karshen yakin kwanaki 33 tsakanin kungiyar Hizbulla da HKI a shekara ta 2006 ya gargadi gwamnatin Isra’ila da ta dakatar da keta hurumin kasar Labanon, amma ta take wannan kuduri ta ci gaba da keta hurumin kasar ta sama da kasa da ruwa.
Majiyar labaran kasar Labanon ta bayyana cewa a daren jiya ma jiragen yakin HKI sun yi shawagi a sararin samaniyar garin Tyre na tsawon lokaci kana kuma ya sauko kasa- kasa a sararin samaniyar birnin Berut da hakan keta kudurin majalisar dinkin duniya ne,
Ana sa bangaren shugaban kasar Labanon Michel Aoun yayi tir da wannan matakin na Isra’la na wuce gona da iri, yace barazanar da suke fuskanta daga Israila shi ne babban abin ya damu gwamnatin kasar Labanon.
Ministan harkokin wajen kasar Labanon ya dade yana kai koke gaban majalisar dinkin duniya da ma kwamitin tsaro game da keta hurumin sararin samaniyar Kasar da Isra’ila ke yi ba dare ba rana.
Wannan yana zuwa ne bayan da kungiyar Hizbullah ta aike da jirgin sama mara matuki a yankin falasdinu inda ya kammala shawagi ya je ya dawo ba tare da Isra’ila ta Ankara ba.