Jiragen Yakin HKI Sun Kai Wasu Hare-hare A Yankin Gaza.
Da Asubahin yau Talata jiragen yakin HKI sun kai jerin Hare-hare a yankin Gaza akan cibiyoyin kungiyoyin gwagwarmaya.
Har ila yau hare-haren na ‘yan sahayoniya sun shafi wasu yankuna na fararen hula a gabacin Khanyunus da makamai masu linzami guda hudu.
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Falasdinawa “Hamas” ta sanar da cewa ta harba makamai na kakkabo jirage a yayin da suke kai wa yankin harin.
Sojojin HKI sun ce; Daya daga cikin jiragensu ya illatu sanadiyyar harbinsa da aka yi da manyan bindigogi.
Tuni dai aka ji karar jiniyar gargadi tana tashi a matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna da suke a gefen Gaza.
READ MORE : Kwanakin Uku A jere Yahudawan Sahayoniya Suna Yin Kutse A Cikin Masallaci Quds.
Harin na ‘Yan sahayoniya yana zuwa ne dai a lokacin da a can birnin Quds su ke ci gaba da keta hurumin masallacin Kudus mai albarka.
READ MORE : Hadaddiyar Daular Larabawa ta amince da gina unguwar Yahudawa gaba daya!
READ MORE : Tashe-tashen hankula a birnin Quds ya kara matsin lamba kan gwamnatin hadin gwiwa a Isra’ila.
READ MORE : Ambaliyar Ruwa A Afirka Ta Kudu Ta Yi Sanadin Mutuwar Sama Da Mutum 400.