Kamfanonin sufurin jiragen sama a najeriya sun sanar da dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin mai zuwa sakamakon tashin gwauron zabbi da man jirgin sama ya yi zuwa Naira 700 a kan kowace lita, su na mai jajantaw fasinjoji.
Sun bayyana haka ne a cikin wata wasika da shugaban kungiyar masu kamfanonin sufurin jiragen sama, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, ya aike wa da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.
A cikin wasikar Sarina ya ce man jiragen sama ya tashin daga Naira 190 duk lita zuwa naira 700 a yaanzu, inda ya ce babu wani kamfanin sufurin jirgen sama da zai iya jure wannan karin frashi.
‘Yan Najeriya sun shiga zaman zullumi sakamakon kudirin karin farashin albarkatun man fetur da hukumomin kasar suka dauka, lamarin da ya janyo tada jijiyoyin wuya tsakaninta da kungiyoyin kwadago.
A halin yanzu dai ana sayar da litar man diesel, wanda akasarin manyan motocin daukar kaya ke amfani da shi a kan sama da naira dari 6, lamarin da ya haddasa tsadar farashin kayayyakin masarufi a kasar.
A wani labarin na daban Gwamnatin Najeriya tace sabon kamfanin jiragen ta da aka yiwa suna Nigeria Air zai fara aiki daga watan Afrilun shekara mai zuwa bayan dogon tsaikon da aka samu.
Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya sanar da cewar wani kamfani ne zai kula da hada hadar jiragen, wanda gwamnati zata zuba jarin kashi 5 a cikin sa, sai kuma wasu ‘yan kasuwar zasu zuba kashi 46, yayin da za’a sayarwa sauran mutane masu bukatar sanya hannun jari kashi 49.
Hadi yace idan kamfanin ya fara aiki zai samar da ayyukan yin ga mutanen da zasu kai 70,000.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ministan sufuri Hadi Sirika
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ministan sufuri Hadi Sirika © Nigeria presidency
Najeriya ta dade tana kokarin kafa kamfanin jiragen sama amma kuma wasu matsalolin cikin gida sun hana ta samun nasara.
A shekarun da suka wuce, gwamnatin Najeriyar ta gabatar da shirin kafa kamfanin jiragen a wani bikin da aka yi a birnin London, amma kuma daga bisani sai aka dakatar da shirin.
A shekarun 1970 Najeriya ta kafa kamfanin Nigeria Airways wanda yayi fice a nahiyar Afirka amma daga bisani sai ya durkushe, abinda ya sa gwamnati ta sayar da kadarorin sa ta kuma dakatar da shi baki daya.
Kasashen Afirka da dama na da kamfanin jiragen sama mallakar kan su wadanda suke matukar tasiri wajen zirga zirga a cikin Afirka da kuma kasashen duniya saboda kyakyawan tsarin yadda ake tafiyar da su.
Daga cikin irin wadannan kamfanoni akwai Ethiopian Airline na kasar Habasha da Kenyan Airline na kasar Kenya da Egypt Air mallakar kasar Masar da South African Airline mallakar Afirka ta Kudu da kuma Maroc Air mallakar kasar Morocco.