Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Juma’a ya yi jawabi a wurin taron da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar(CPPCC) ta shirya don yin maraba da shekarar 2024.
Xi Jinping ya jaddada cewa, ciyar da babban aikin gina kasar Sin mai karfi gaba, da farfado da ita daga dukkan bangarori, ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin shi ne babban aikin jam’iyyar da na kasar kan sabuwar tafiya a wannan sabon zamani.
Kaza lika, Xi Jinping ya yi kira da a karfafa hadin kan ‘yan kishin kasa daga bangarori daban daban, da samar da manyan nasarori ta hanyar yin aiki tukuru, da kuma rubuta sabon babi kan zamanantar da kasar Sin tare. (Yahaya).
A wani labarin na daban daga karshen watan Agusta aka rika yada jita-jitar bayyanar wasu mata da suke shiga gidajen mutane wadanda ake musu lakabi da ‘masu shan jini’ a wasu sassa na Arewa musamman Jihar Kano.
An ce wadannan mutane suna yawo ne gida-gida a lokacin da ska tabbatar da mazaje ba sa gida, inda da zarar sun shiga, abin da suke fara nema shi ne a taimaka musu da ruwan sha ko wani abu, wanda kuma da an taimaka musu da abin da suka bukata, to wacce ta ba da taimakon sai a ga ta yanke jiki ta fadi, daga nan lamarin ya kai ga ta rasa ranta.
Masu yada maganganun sun ce irin wannan ibtila’i ya faru a unguwanni daban-daban a cikin Birnin Kano.
A wasu bidiyo da suke yawo a kafofin sadarwa na zamani ana ganin yadda ake dukan wadannan mata yayin da aka kama su, sannan kuma a lokacin da ake yi musu tambayoyi sukan kasa ba da wata gamsasshiyar amsa da za ta fahimtar da mutane yadda gaskiyar lamarin yake.
An samu irin wannan lamarin a unguwannin Hotoro, Zango, Rijiyar Lemo, Gwagwarwa, Kwana Hudu Medile, da sauran wasu unguwanni da ke cikin birnin Kano.
Baya ga haka, akwai wani bidiyo da yake yawo na wasu mata ‘yan kauye da aka nuna wasu matasa na yi musu tambayoyi, amma su kuma maganarsu ba irin ta ‘yan Jihar Kano ba ce mutanen Sakkwato ne.
Sannan akwai wani bidiyo na wata baiwar Allah da lamarin ya shafi ‘yarta wacce ‘yar ba ta kai shekara guda da haihuwa ba, inda uwar take bayanin yadda ta rasa ‘yarta ta irin wannan hanya.
Kamar yadda LEADERSHIP Hausa ta bi diddigi, tun da farko daga yankin Kankara da ke Jihar Katsina aka fara samun bullar irin wannan labari, inda aka ce wata tsohuwa ta shiga wani gida inda ta bukaci a taimaka mata da ruwa ta shiga ban daki, shigarta ke da wuya sai matar gidan ta fadi.
A cewar labarin sai jini ya fara kwarara daga jikin matar, daga nan sai ita bakuwar ta kama hanyar ficewa daga gidan a kan hanyar fita suka ci karo da mijin matar, tun da bai san abin da ke faruwa ba sai ya bar ta ta wuce, yana shiga gida sai ya tarar da matarsa cikin jini, hakan tasa ya dawo da gudu, ya nemi gudunmawar al’umma aka kama matar. Bayan yi mata tambayoyi sai ta bayyana cewa su 100 aka turo Jihar Katsina, yanzu haka an kashe tara daga cikinsu, ita ce ta goma. In ji majiyarmu.
Sakamakon yadda lamarin ya yi kamari a tsakanin al’umma, LEADERSHIP Hausa ta gudanar da Shirin Tattaunawa ta Manhajar Twitter Space, inda ta gayyato mai magana da yawun ‘yansanda, reshen Jihar Kano, SP Haruna Abdullahi Kiyawa da kwararriyar mai horarwa da warware mishkilar zamantakewa, shugabar Cibiyar Nurul Huda, Hajiya Fatima Bamalli domin warware zare da abawa kan wannan al’amari.
A jawabin da ya yi, SP Haruna ya tabbatar da wannan jita-jita da ake yadawa inda ya ce tuni rundunarsu ta kaddamar da bincike, yana mai cewa, “Mun samu rahotanni 14 cikin kwana 5 na rufar wa mata da zargin ‘yan shan jini ne, kamar a unguwar Hotoro an samu guda uku, Zango 4,” in ji shi.
“Duk mun gudanar da bincike daya bayan daya, duk binciken da muka yi ba mu samu ko daya a cikin matan da ake zargi da laifin shan jini ba, abu ne na Allah wadai.
A Unguwar Kwana 4, wasu ‘yan mata ne suka kai caji a wani gida, kawai daya ta ce wa matar gidan za ta je bandaki sai matar ta kwarma ihu wai budurwar ‘yar shan jini ce, shi kuma maigida da ya zo maimakon ya yi amfani da hankali kawai sai ya kulle ‘yan matan a daki,’yan unguwa suka taru, matar gidan ta daki wadda take zargin, ‘yansanda ne suka kubutar da su.
A nata bangaren, Shugabar Cibiyar Horarwa ta Nurul Huda, Hajiya Fatima Bamalli Bamalli ta yi bayanin cewa,
“Ana ta yadawa muna ganin bidiyos, ana ce wa mutane a daina ba da taimakon ruwan sha kuma a daina bude kofar gida. Gaskiya kowane Dan’adam akwai yakininsa. Da aka fara yadawa, na ce wannan tsafi ne amma ni ban yarda da shi ba.
Na daya dai, mu mata daga mahangar addini, Allah ya umarci Manzon Allah ya fada wa muminai a killace mata a gida. Kuma haka nan mata a yanzu ana business ana aiki amma ya kamata a yi bisa sharuddan addini. Abin da ya sa abin ya fi faruwa da mata saboda mu ne muke da sakaci, Wasu make-up da ake yi mara ma’ana, to mai yin irin wannan ne ma abin zai iya kamata. Sannan an manta da yin azkar da addu’o’i shi ya sa ma idan an yi abin zai kama mutum.
“Ni dai ban yarda da abin ba dama. Ba na jin akwai wanda zai zo ya ce na ba shi ruwa na hana shi. Idan ka ciyar ko ka shayar Allah zai ba ka lada. To don me za a hana mutane yi? Ni da nake son yin taimakon saboda Allah ba na tunanin wani abu zai faru in ba alheri ba. Ya kamata mu koma wa wayewar addinin musulunci ba na bature ba kawai. Idan kuma kina azkar wani abu ya faru to ka sani wannan jarrabawa ce kawai. Kuma Allah na iya sa haka ta zama kaffara.” In ji ta.
Source: LEADERSHIPHAUSA