Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umarnin gudanar da bincike tare da ceto mutanen da suka bace a bala’in ambaliyar da ya afku a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Xi ya kuma bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da karfafa sa ido kan tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wani dan takaitaccen ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a makon da ya gabata ya haifar da bala’i min indillahi a wurin aikin gina wata babbar hanya da ke kusa da kogi a gundumar Jinyang a yankin Liangshan mai cin gashin kansa na kabilar Yi na lardin Sichuan. (Mai fassara: Yahaya)
Source: LEADERSHIPHAUSA