Jeffery Shaun King mai shekara 44 ya sanya da shigar Falasɗinawa ta hirami da kwarkwar, yayin da yake jawabi ga taron, inda ya ce ya yanke shawarar shiga Musulunci ne bayan “wata shida da suka gabata na wahala da raɗaɗi da tashin hankalin da muka gani a Gaza”.
Marubuci kuma ɗan gwagwarmaya Jeffery Shaun King da matarsa Rai King sun musulunta a ranar farko ta watan Ramadan.
Marubuci kuma ɗan gwagwarmaya Jeffery Shaun King da matarsa Rai King sun musulunta a ranar farko ta watan Ramadan.
Su biyun sun karɓi shahada a ranar Litinin inda aka watsa kai tsaye a shafin Instagram, ƙarƙashin jagorancin abokin King na sama da shekaru 10 – malamin Musuluncin nan na Amurka Omar Suleiman.
King mai shekara 44 sanye da shigar Falasɗinawa ta jallabiya da hirami, yayin da yake jawabi ga taron, ya ce ya yanke shawarar shiga Musulunci ne bayan “wata shida da suka gabata na wahala da raɗaɗi da tashin hankalin da muka gani a Gaza”.
“Abin ya taɓa ni sosai ganin mutane a yanzu a cikin mafi haɗari da wuri mai ban tsoro a duniya ba sa iya kallon komai sai tarkace da ragowar danginsu, kuma har yanzu suna ganin ma’ana da manufa a rayuwa.”
“Ba ni kaɗai imaninsu da miƙa wuyansu ga Musulunci ya buɗe wa zuciya ba, ya buɗe zuciyoyin miliyoyin mutane a faɗin duniya,” a cewar King.
King ya kasance mai yawan bayyana ra’ayi da nuna goyon bayansa ga Falasɗinu a kan yaƙin da take yi da Isra’ila a Gaza da aka yi wa ƙawanya, wanda ya kashe aƙalla mutum 31,112, mafi yawansu yara da mata, sannan zuwa yanzu mutum 72,760 sun jikkata.
Tun ranar 7 ga watan Oktoba, King yake wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda ake lalata Gaza, tare da yin kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila.
King har sai da ya yi ikirarin cewa ya yi aiki da ƙungiyar Hamas don a saki Amurkawa biyu da aka yi garkuwa da su: Natalie Raanan mai shekara 17 da mahaifiyarta Judith Tai Raanan mai shekara 59. Ikirarin da iyalansu suka musanta.
A martanin da ya yi na goyon bayan Falasɗinu da yake yi, King ya ce Instagram sun rufe shafinsa mai yawan mabiya sama da miliyan shida a watan Disamba. Har yanzu ba a san dalilin da ya sa kamfanin Meta suka rufe shafin King ba.
To amma wane ne Shaun King kuma me ya sa yake fafutukar kare Falasɗinawa?
Ya Sha Fama Da Wariya Da Kalaman Tsana
Daga yadda gungun matasa suka taɓa yunƙurin taka shi da motar ɗaukar kaya a makaranta zuwa yi masa tiyatar ƙashin baya saboda harin da ɓata-gari da ake kira “rednecks” suka kai masa, King yana yawan magana kan nuna wariyar launin fata da ya fuskanta a lokacin da yake yaro a matsayinsa na ɗan wata ƙabilar daban da ya girma a jihar Kentucky ta Amurka.
Bayan wani hari da aka taɓa kai masa, King ya ce wata ziyara da babban abokinsa na makarantar sakandare da babansa, wanda fasto ne, suka kai masa, ta sa shi fara tunanin samun abin yi a addini.
King ya ce ya girma a matsayin maraya kuma “ziyarar da wannan mutum ke kai mini ta sa na ji ina son zama kamar sa.”
Bayan kammala karatunsa, King ya ɗan yi koyarwa a makarantar sakandare da kuma fannin shari’a, kafin daga baya ya zama fasto a wata coci a Georgia.
A shekarar 2008 ne ya kafa coci a Atlanta da ake kira Courageous Church, kuma yana yawan amfani da shafukan sada zumunta wajen shigar da mutane addinin, har ma ake yi masa laƙabi da “Faston Facebook.”
Sai dai kuma, bayan shekaru huɗu kawai sai ya yi murabus daga coci saboda “damuwa da gajiya.”
Fafutuka don kare hakkin jama’a
Duk tsawon lokacin, yana yin la’akari da abubuwan da ilimin da ya koya da suka shafi laifukan nuna ƙiyayya, King ya sadaukar da rayuwarsa don inganta al’amuran zamantakewa, musamman a fafutukar tabbatar da cewa rayuwar baƙaƙen fata na da muhimmanci, wato “Black Lives Matter Movement.”
Ya yi hakan ne ta hanyar rubuce-rubucen da suka mayar da hankali kan ‘yancin ɗan’adam da ƙabilanci da zaluncin ‘yan sanda da ɗaure jama’a da kuma rashin ɗa’a.
Yana yawan rubuce-rubuce a kafafen watsa labarai kamar su Daily Kos da the New York Daily News da kuma The Young Turks.
A wata maƙala ta musamman, King ya yi nazari kan harbin matashin baƙar fata Michael Brown da aka yi, kuma ya yi jayayya da ikirarin da aka yi cewa ran ɗan sanda Darren Wilson na cikin haɗari ne shi ya sa ya harbe matashin.
An kuma yaba masa a matsayin wanda ya jagoranci wata fafutuka a kafofin sada zumunta wadda ta kai ga ganowa da kama mutane uku daga cikin mutanen da suka kai hari kan baƙar fata DeAndre Harris a cikin 2017.
Ta hanyar gwagwarmayarsa, King kuma ya kafa wata ƙungiya mai zaman kanta, Grassroots Law Project, kuma ya fara kamfen na intanet a shafuka da yawa ciki har da ƙaddamar da shafukan HopeMob.org da Justice Together da Real Justice PAC da The North Star.
Duk da haka, wasu ayyukan nasa sun fuskanci zarge-zarge na rashin gudanar da kasafin kudi da ƙorafe-ƙorafe daga abokan aikinsa tsawon shekaru.
DUBA NAN: Bukatar Tinubu Ta Bawa Ma’aikatan Jihohi Kyauta
King da matarsa a halin yanzu suna zaune a New York tare da ’ya’yansu biyar, biyu daga cikinsu riƙonsu suke yi.