Jeff Bezos Mamallakin Amazon Ya Caccaki Biden Kan Matsalar Hauhawar Farashin Kayayyaki.
Mutumin da ya kafa Amazon Jeff Bezos ya ce; Joe Biden ko dai yana yaudarar jama’a ne ko kuma ya rasa fahimtar tattalin arziki, bayan da shugaban na Amurka ya yi kira ga kamfanonin da ke tafiyar da gidajen mai da su rage farashin iskar gas.
Yana da matukar mahimmanci ga Fadar White House ta rika tantance maganganun da suke fitowa daga cikinta, daga ciki hard a irin wannan furuci na Joe Biden, domin kuwa ko dai ya yi wannan magana ne saboda jin kai da kasaita, ko kuma saboda rashin sanin harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
Biden ya yi kira kai tsaye ga kamfanonin da suke tafiyar da gidajen mai a cikin wani sakon twitter a ranar Asabar, inda ya karfafa musu gwiwa da su rage farashin iskar gas, yayin da farashin iskar gas ya yi tashin gwabron zabi a kasar ta Amurka.
“Sakona zuwa ga kamfanonin da ke gudanar da gidajen mai, ku sanya farashi mai sauki a fanfo mai, wannan lokaci ne na yaki da kuma hadari a duniya.” Inji Joe Biden.
Ko a baya Jeff ya caccaki Biden, kana bin da ya kira rashin sanin yadda ake tafiyar da siyasar tattalin arziki a Amurka.